Pages

Friday 23 December 2016

Policeman Stationed At Zenith Bank Zaria Shoots His Colleague & Two Civilians


From the little I understood from the story(I am not good in Hausa),a policeman on Friday shot his colleague at Zenith Bank in Sabon Gari LGA,Zaria.Two Civilians were also shot by the police in what appears to be a riot.Below is the Hausa narration of the story,our Hausa readers should please explain more'Dan Sanda Ya Harbe Abokin Aikinsa A Zariya

Daga Ammar Muhammad Rajab

Wani abu mai kama da al'amara ko ban mamaki ya auku a garin Zariya a yau Juma'a. Al'amarin ya auku ne a daidai bakin Bankin Zenith dake PZ a karamar hukumar Sabon Garin Zariya a inda kwatsam aka ga 'Dan Sandar kwantar da Tarzoma wato Mobile Police dake Gadi a Bankin ya fara harbe-harben kan mai Uwa da Wabi, nan take ya harbe dan uwansa 'Dan Sanda. Abin ya fara ne a lokacin da Dan Sandan ya fara cacar baki da wani Soja akan wani abu da har yanzu ba a san dalili ba. Jim kadan da wannan, sai kawai aka ga 'Dan Sandan ya koma tsakiyan titi ya fara harbe-harben kan mai Uwa da Wabi.

Yana cikin wannan harbe-harben wanda ya tarwatsa kowa akan titin, kuma yana bi da gudu yana harbi, sai ga 'Yan Sandan Operation Yaki sun iso wurin, a inda suka yi musayar wuta tsakani, daga bisani suka ci galabansa. Suma al'umma dake wurin, sun rika jifansa da duwatsu domin a samu ya daina harbin. Bayan ya kai kasa, a gaban 'Yan Sandan Operation Yakin, mutane suka rika bugunsa da Gora da kuma duwatsu, su kuma 'yan Sanda na kokarin hanawa har suka samu suka kwashe shi da wadanda ya harba a mota.

Sai dai wani ganau ya shaida min cewa; "da farko da muka ji harbe-harben, mun dauka 'Yan Fashi ne suka zo Bankin, sai daga baya muka ga ashe haka nan yake harbe-harben, muna ganin da alama ya yi shaye-shaye ne, ba cikin hayyancinsa yake ba."

Har wala yau, wani ganau ya tabbatarwa da wakilinmu cewa; baya ga 'Dan Sandan da aka harba, har wala yau ya harbi fararen hula mutum biyu. Ya zuwa hada wannan rahoton, har yanzu bangaren 'Yan Sanda ba su ce uffan ba, hakazalika ma ma'aikatan Bankin na Zenith'


No comments:

Post a Comment